Yau Alhamis ne Allah yayi wa Sarkin Deba Abubakar Waziri rasuwa a wata asibiti dake Abuja.
Sarkin ya rasune bayan fama da rashin lafiya da yayi.
Marigayi Abubakar Waziri ya shekara 33 akan karagar mulkin masarautar Deba.
Ya rasu yana da shekaru 79 a duniya sannan shine sarki na 36 a jerin sarakunan masarautar Deba.