Ali Nuhu zai shugabanci tallata kamfanin Telecom Consumer

0

Jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu zai shugabanci tallata kamfanin Telecom Consumer wanda za’a fara daga 15 ga watan Maris a Abuja.

Ali Nuhu ya sanar da hakan ne a shafinsa na Instagram wanda darektan hudda da jama’a na hukumar sadarwa na Najeriya wato ‘Nigerian Communications Commission’ Tony Ojobo ya tabbatar da hakan.

Ojobo ya ce kamfanin ta gyara kafofin sadarwan ta inda mutane za su iya amfani da shi wurin hana sakonnin da ba su bukata shigowa wayoyinsu sannan kuma sun bada wata lambar wayan tarho kamar haka 622 domin ganawa da su kai tsaye.

Ya kuma ce suna fatan cewa tallan zai taimaka wajen samun hadin kan kamfanonin.

Ali Nuhu na daya daga cikin manyan‘yan wasan da suka zama jarumai a farfajiyar fina-finan Hausa da Fina-finan turanci ne.

Share.

game da Author