Aisha Buhari ta ba da kyautar motar asibiti na tafi da gidanka

0

Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari taba da kyautar wata motar asibitin tafi da gidanka domin taimakawa domin kula da lafiyar mutanen karkara.

Ta bada da motar ne a garin Abuja ranar Laraba.

Ta ce wannan shirin na daya daga cikin aiyukan da gidauniyar ta mai suna future Assured ta ke yi domin taimakawa talakawa musamman mazauna karkara a kasa Najeriya.

Kamar yadda wani babban jami’I a gidauniyar Future Assured Kamal Mohammed ya yi bayani akan yadda motar take aiki, yace a motar akwai magunguna, dakin ganin likiti da gudanar da gwaji da bada agaji na gaggawa.

Daga karshe ta ce gidauniyar na shirin bunkasa irin wannan aiyuka zuwa sauran jihohin dake kasan domin suma su amfana da aikin gidauniyar.

Mobile Car 3

Mobile car 2

Mobile Car

Share.

game da Author