AIKIN HAJJI: An rage kudin gidajen zaman mahajjatan bana

1

Hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa ta sanar da rage kudin gidajen da mahajjatan bana za su biya a lokacin aikin hajji.

Hukumar ta ce hakan ya yiwu ne bayan tattaunawa da tayi da masu gidajen da take shirin kamawa ‘yan Najeriya a hajjin bana.

Kakakin hukumar Uba Mana ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar yau.

A dalilin haka mahajjata zasu biya kasa da riyal 500 zuwa 900 a garin Makka sannan kuma su biya kasa da riyal 614 a Madinah a hajjin 2017.

Yace za’a samu ragin sama da Dala Miliyan $12 ganin tattaunawar da sukeyi akan hakan a gidajen Madinah.

Uba yace zasu biya kudaden gidajen ne bayan sun tabbatar da kyan gidan da kuma kusancinsa da harami bakamar yadda akeyi da ba ace wai ga kayyadadden Kudi da za’a biya.

Share.

game da Author

  • Abdulsamad muh,d sani zwall

    Allah ya kara wa babanmu kuma shugabanmu lfy, allah yasa daga yanzu har zuwa in ma sha allahu kayi ta mulkin kasan nan mahasada sai su mutu, baba buhari ajiyan allah maga nin kanana kwari, mahajjatanmu allah ya dawo mana daku lfy, da saura mahajjatan duniya baki daya, naka danka kuma jikanka masoyinka har abada insha allah,