Abubuwa uku da tsaftace muhalli ke kara wa ‘ya’yan ka

0

Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta ce rashin tsaftace muhalli na kawo mutuwan yara kanana musamman yaran dake kasa da shekara biyar.

A bayanan rahoton hukumar, sama da kananan yara miliyan 1.7 ke mutuwa saboda rashin tsaftatacen ruwan sha, rashin tsaftatace muhalli da shakan iskan dake kawo lahani a jiki kamar hayakin taba da hayakin icen da ake Konawa.

Rahotan ya nuna cewa tsaftace muhalli, shan tsaftatacen ruwa da guje wa hayakin da ke kawo lahani a jikin mutum na kare mutum daga cututtuka kamarsu zazzabin cizon sauro, cutar huhu,cutar amai da gudawa wanda ya fi kama yara kanana musamman ‘yan kasa da shekara 5.

Darekta Maria Neira na hukumar ta kara ba da bayanai akan yadda za a iya ceto rayukan yara kananan ta hanyoyi kamar haka:

1. Tsaftace muhalli wanda ya hada da kawar da ruwan dati, cire ciyawa da kuma kona bola domin kare yara daga kamuwa da cutar zazzabin cizon Sauro, cutar huhu da kuma sauran su.

2. Mata masu dauke da juna biyu su yi kokarin nisantar shakan gurbataccen iska domin kariya a garesu da dan da suke dauke da shi musamman wajen girki.

3. Shan tsaftatacen ruwa zai kare ‘ya’yanka daga kamuwa daga cutar kwalara.

Share.

game da Author