Sarkin musulmi yayi kira ga gwamnati da a sassauta game da dokar hana shigo da abinci

0

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya shawarci gwamnatin tarayya da ta sassauta dokar hana shigo da shinkafa da kuma motoci ta iyakokin kasa Najeriya.

Ya fadi hakan ne lokacin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai masa ziyara a fadarsa dake Sokoto.

Ya ce kamata ya yi gwamnati da fitar da mamufofin da za su rage wahalhalun da mutanen Najeriya ke fama da shi musamman sassautar dokar hana shigo da shinkafa da motoci amma ba shirye-shiyen da za su kara tura mutanen kasa cikin wahala ba.

Ya kuma kara da cewa zai cigaba da taimakawa wa gwamnati da addu’o’I da shawarwari nigari domin samun cigaba a kasa Najeriya.

Osinbajo ya gode wa Sarkin Musulmi Sa’ad da irin gudunmawar da yak e ba wannan gwamnati sannan kuma yace gwamnatin su za su kara kaimi akan wadata jihar Sokoto da taimakon da zata bukata domin bunkasa harkar noma a jihar.

Share.

game da Author