Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce gwamnatin sa zata biya duk wanda ya fallasa mai yada jita-jita a jihar.
Gwamnan yace zai biya wanda yayi wannan fallasan naira 500,000.
Gwamnan ya ce ya zama dole gwamnati ta yi irin wannan sanarwa saboda yada jita-jita da ke tayi a jihar a dan kwanakinnan ya sa ana zaman dar-dar a wasu sassan jihar.
Gwamnatin ta nuna rashin jin dadinta kan yadda wasu ‘yan siyasa ke yin amfani da zauna gari banza wajen biyansu kudaden domin su yada jita-jita a jihar.
Ya ce yin hakan da gwamnati tayi zai rage yawan mugun iri a tsakanin mutanen jihar sannan ya sa kowa ya shiga taitayinsa.
Gwamna Yahaya Bello yace gwamnati zata biya mutum kudin nan take idan har ya fallasa irin masu yada jita-jitan da zai kawo tashin hankali a jihar.
” Zan biya 500,000 nan take idan aka bamu bayanai masu gamsarwa”
Wani dattijo a jihar yayi kira ga gwamnan da ya abin a hankali domin fadin irin hakan da yayi zai iya tauye wa mutane ‘yancin su na fadin kowace irin magana kuma ya kawo rudani a jihar.
Dattijon ya ce ya yi ta kokarin nuna wa gwamna Yahaya irin mutanen da ya kamata ya nada domin taimaka masa amma yaki ji. Gashi nan yanzu saboda rashin kwararru ya sa yana ta tafka tabargaza wajen gudanar da mulkinsa a jihar.
Dattijon ya ne mi a boye sunansa saboda kusancin sa da gwamnan jihar Yahaya Bello.
Mai ba gwamnan Bello shawara akan sababbin kafafen yada labarai Gbenga Olorunpomi yace gwamnati tayi hakanne domin gano masu neman ta da zaune tsaye a jihar musamman ganin cewa jihar tayi iyakoki da jihohi kusan tara saboda haka dole ne a nemi bayanai ko da na baki ne ballantana masu son tada zaune tsaye.
Gbenga ya ce gwamnati ba za ta sa ma wani iyaka ba kan ‘yancinsa na fadin magana da doka ta bashi.