Za’a karo taragon jirgin Kasa domin jigilan matafiya daga Kaduna zuwa Abuja

0

Gwamnatin Najeriya ta amince da a karo sababbin taragon jirgen kasa domin jigilan matafiya daga Kaduna zuwa Abuja.

Ministan Sufuri, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan wa manema labarai a fadar gwamnati dake Abuja.

Ministan yace gwamnati tayi hakanne ganin yadda matafiya zasu karu musamman daga Kaduna zuwa Abuja nan da wata mai zuwa a dalilin gyaran filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja da za’a fara.

Filin jirgin saman Kaduna ne za’a yi amfani dashi domin hada-hadan jiragen sama wanda hakan yasa za’a samu Karin yawan mutanen da zasu dinga bin hanyar daga Kaduna zuwa Abuja da kuma Abuja zuwa Kaduna.

Kwanakin baya gwamnati ta bada kwangilan gyaran hanyar Kaduna zuwa Abuja duk saboda hakan.

Share.

game da Author