Shugaban gidauniyar ‘Bill da Melinda Gates’ Mairo Mandara ta ce kawar da cutar shan inna a kasa Najeriya abu ne da gidauniyar ta sa a gaba kuma za tayi matukar farinciki idan ta samu cimma wannan buri na ta.
Mairo ta yi bayanin cewa kasashen Najeriya, Pakistan da Afghanistan ne kadai suka rage basu gama kakkabe cutar a kasashensu ba, saboda haka gidauniyar take iya kokarinta domin ganin ta kawar da cutar a kasa Najeriya zuwa karshen wannan shekara.
Ta kara da cewa bayan kawar da cutar shan’inna da suka sa a gaba gidauniyar na kokarin ganin cewa ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya a Najeriya.
Ta ya bayanin cewa kafin bullowar cutar shan’inna a jihar Borno, kasa Najeriya ta yi shekara biyu a jere babu rahoton wani ya kamu da cutar.
Ta kuma ce za su tallafawa manoman kasa Najeriya domin samun nasara akan hakan.
Mandara ta ce gidauniyar Bill da gwamnatin Najeriya za su hada kai domin koyar da mutane musamman uwaye mata akan yadda zasu kare kansu daga kamuwa daga wasu cututtuka da basu sansu ba ma.