Za mu gyara ofishin mu a karshen makon nan domin fara aiki – Inji Ali Modu

0

Halartaccen shugaban jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff yace za’a kawo ma su gyara domin su duba irin gyare-gyaren da ya kamata ayi a shelkwatar jam’iyyar da ke Abuja a cikin hutun karshen wannan mako.

Ali modu Sheriff ya fadi hakanne a lokacin da ya halarci ofishin jam’iyyar ranar Alhamis.

Yace ofisoshin jam’iyyar suna neman gyara sannan wasu sashe na ginin ofishin na bukatar fenti.

Y ace zai turo ma’aikata a karshen makon nan domin su duba sannan a fara aiki.

Ali Sheriff yace za su dawo aiki gadan-gadan ranar Litini ko Talata.

Wadansu daga cikin jigajigan jam’iyyar PDP kuma magoya bayan bangaren Ali Modu da suka hada da Cairo Ojougboh, Wale Oladipo, Buruji Kashamu, da Ahmed Gulak ne suka raka shi ofishin.

Share.

game da Author