Jam’iyyar PDP a jihar Katsina yau tayi kamun sama da ‘ya’yan jam’iyyar APC 1500 daga garin Radda dake karamar hukumar Charanchi jihar Katsina.
Shugaban tawagar Mustapha Radda ya ce bautar da suka yi wa jam’iyyar APC a jihar ya isa haka.
Yace dukkansu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da suka gaji da yi mata bautar da babu riba.
Ya kara da cewa wadansu ne dabam suke morewa APC a jihar ba su da sukayi mata bauta ba.
Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Salisu Majigiri ya ce jam’iyyar PDP din na maraba da su sannan kuma jam’iyyar za ta basu iko da dama kamar dasu aka kafa jam’iyyar a jihar.