Kwamishin rundunar ‘yansandan jihar Kaduna Agyole Abbey ya sanar da Kama wadansu mutane su biyar a hanyarsu na kai hari wasu kauyuka dake kusa da Samarun Kataf, Kudancin Kaduna.
Kwamishina Abbey, ya ce jami’ansa sun kama mutanen ne a hanyarsu na zuwa kauyukan.
Ya ce an Kamasu ne a cikin wata mota kirar Golf dauke da bindigogi kirar AK47, da layu da kuma kudi da ya kai naira 86,000.
Abbey ya kara da cewa jami’ansa sun sami nasaran hakane a dalilin sintiri da suke yi a dazukan da ke kauyukan yankin domin ganin an kawo karshen rikicin yankin da yaki ci yaki cinyewa ranar Alhamis.
Yace nan ba da dadewaba za’a gurfanar da wadanda aka kama din a gaban Kuliya.