‘Yan Najeriya 41 ne kasar Ingila ta dawo dasu yau

1

Yau Laraba ne Kasar Ingila ta dawo da wadansu ‘yan kasa Najeriya kimanin su 41 zuwa filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Legas.

Da yake sanar da hakan, shugaban hukumar bada agajin gaggawa na kasa (NEMA) Muhammed Sani Sidi yace an taso keyar yan Najeriyan ne a dalilin laifuffukan da ya shafi shiga da ficen kasar.

Sani Sidi yace maza 33 ne da mata 8 aka dawo dasu a wata jirgin saman haya daga kasar Ingila din.

Ya kara da cewa hukumar NEMA ta zo filin jirgin saman ne domin ta tarbe su da yi musu maraba da dawo kasa Najeriya.

Ya ce gwamnati za ta basu dan kudin kashewa da na mota kowa ya karusa inda ya fito domin cigaba da rayuwa.

Share.

game da Author