‘Yan kunar bakin wake sun tada bamabamai a Maiduguri

1

Mutane 11 ne suka rasa rayukansu a wadansu hare-haren bamabamai da ‘yan kunar bakin wake suka yi a garin Maiduguri.

Dukkansu sun mutu a harin.

3 daga cikin ‘yan kunar bakin waken wanda mata ne sun tada nasu bamabaman ne a kusa da tashan motar Muna.

Wani mazaunin unguwan yace mutane biyu ne suka rasa rayukansu a wannan hari.

Motocin haya da dama sun kone a sanadiyyar harin.

‘Yan banga 7 ne suka ji raunuka a harin sannan wasu motocin kaya da sukayi lodi zuwa bakin iyakar jihar da kasar Chadi duk sun kone.

Bayan ‘yan kunar bakin waken sun tada bamabamai sojoji sun bude musu wuta inda suka kashe su duka tare da wadansu yan bindiga da sukayi musu rakiya a kan Babura zuwa garin na Maiduguri.

Rundunar ‘yan sandan jihar Barno ta tabbatar da harin.

Karanta labarin a shafin mu na turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-Wdr

Share.

game da Author