Ciwon ido wanda aka fi sani da GLAUCOMA ya addabi mutane a kasa Najeriya wanda babban abun tashin hankali akai shine mutane da dama basu san cewa cutar bane ke damun idanuwarsu.
Bincike ya nuna cewa wannan ciwo na daya daga cikin cututtukar da ke kawo makanta kuma ya fi kama mutanen da suka kai shekara 40 zuwa sama ne.
Cutar na fito wa ne kamar kwantsa a idanuwar mutum wanda idan ba a dauki mataki akansa da wuri ba yakan kai ga makanta.
Likitan ido Nkiru Akaraiwe wanda shugaban kungiyar likitocin ido Sebastine Nwosu ya wakilta ta shawarci mutanen Najeriya da su yi kokarin zuwa asibiti a kalla sau daya a shekara domin gwajin idanuwarsu.
Ta fadi haka ne a wani taron da kungiyar likitocin ido suka shirya a jihar Enugu domin wayar da kan mutane akan cutar na glaucoma.
Ta ce babu maganin da za a sha domin a samu warkewa gaba daya daga cutar amma idan aka gano cutar da wuri ta hanyar gwaji za a iyan shan maganin da zai rage yaduwarta sannan mutum zai kubuta daga makanta farad daya.
Shugaban taron Rich Umeh ya koka ya shawarci likitocin ido da su yi kokarin shiga cikin kauyuka domin wayar wa mutane kai akan yadda za su kare kansu daga cutar na Glaucoma.