Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yace akwai wadansu ‘yan siyasa da ke fatan shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rasu domin su za mo mataimakin shugaban Kasa a Najeriya.
Ko da yake Sanata Shehu Sani bai ambato sunayen wadanda yake nufi da wannan zargi ba ya ce suna da masaniya akan wadannan mutanen.
“Duk wadanda suke ta yada jita-jitan mutuwan Buhari makiyan sa ne kuma sunayin haka ne domin suna so a nada su mataimakin shugaban Kasa. Amma ba za su samu yadda suke so ba domin Buhari zai dawo kasa cikin koshin Lafiya.”
Sanata Shehu Sani ya fadi hakanne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya ziyarci kabari Mal. Aminu Kano dake gidan Mumbaya a Kano.
Yace abin da masu wannan shiri basu sani ba shine shi kansa Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo basu yarda da su wadannan mutane ba duk da suna manne da su.
“ Osinbajo mutum ne wanda shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yarda da shi kuma babu wanda zai sa ko kuma ya zuga shi yayi abinda zai ruguza wannan yarda da ke tsakaninsu.”
Yace Buhari ya na kokarin ganin ya kakkabe duk kurayen da ke wawushe kudaden gwamnati, sannan kuma yace sanin kowa cewa ‘yan siyasa da yawa sun maida siyasa hanyar da mutum zai nemi wata matsayi domin gyara harkokinsa kawai.