Kotu a jihar Gombe ta gurfanar da wani mahauci dan shekara 25 mai suna Shamsudeen Musa da laifin yi ma wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade.
Alkalin kotun mai shari’a Bello Sheriff ranar Alhamis ya bada umurin a cigaba da ajiye Shamsudeen a kurkukun Zirindaza akan laifin da yayi zuwa 1 ga watan Maris.
Ismail Adamu wanda shine ya kai Shamsudden kara ya shaida wa kotu cewa mahaucin ya aikata laifin ne ranar 20 ga watan Janairu da karfe 12:30 na rana.
Ismail ya ce mahaucin ya rudi yariyar ne zuwa wani kangon gini inda ya danne ta da karfin tsiya ya yi mata fyaden.
Ya roki alfarmar kotu da ta daga shari’ar har sai bayan ‘yan sanda sun gama bincike.