Tinubu da Bisi Akande sun ziyarci Buhari a birnin Landan

2

Jagororin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da Bisi Akande sun ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Gidan Abuja dake birnin London.

Bashar Ahmad ne ya sanarda hakan a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari na birnin Landan ne inda yake yin hutunsa na shekara, kuma yake amfani damar inda yake ganin likitocinsa.

Ko a safiyar yau Shugaba Buharin ya kira Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara inda suka yi doguwar tattaunawa kan yadda tsadar kayan abinci ke damun ‘yan Nigeria da hanyoyin da za a bi don magance su.

Share.

game da Author