Kakakin rundunar Sojin Najeriya Sani Usman yace mayakan Boko Haram da yawa ne suka sheka lahira yau a wata batakashi da suka yi da Sojin Najeriya yau.
A wata sanarwa da Sani Usman ya sanya wa hannu, yace sojojin Najeriya 3 ne suka rasa rayukansu a batakashin inda wasu 5 suka sami raunuka dabam dabam.
Ya kara da cewa Sojojin sun kwato makamai masu yawa a hannun mayakan Boko Haram din da ya hada da motocin yaki, bindigogi da harsashai.
Anyi arangamar ne a lokacin da sojojin Najeriya ke cigaba da kakkabe sauran maboyan Boko Haram din a kauyukan Dulsa da Buk dake karamar hukuma, Damboa.