Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yace shi yanzu a shirye yake da su shirya da tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganduje yace sunyi zaman mutunci da Kwankwaso a lokacin da yake gwamnan jihar Kano kuma dalilin haka ne yasa ya gaji Kwankwason.
Yace ya kamata su shirya domin rashin shirin nasu ba abin alfahari bane a garesu duka.
Yace kofarsa a bude take domin a shirya.