Shin ko kasan cewa zukar taba sigari da shan giya na kawo cutar daji? Karanta bayanai anan

0

Shugaban kungiyar likitocin da suka kware wajen kula da kawar da cutar daji Festus Igbinaba ya shawarci ‘yan Najeriya akan yadda za su bi domin kare kansu daga kamuwa da ga cutar daji da kuma da yadda mai dauke da cutar zai kula da lafiyarsa a wannan lokacin.

Shugaban kungiyar ya ce wayar da kan mutane akan yadda zasu kare kansu da yadda ake gano cutar na daga cikin matakai na farko da za’a bi domin kawar da cutar a kasa Najeriya.

Ya ce bincike ta nuna cewa kashi 40 bisa 100 na mafi yawa yawan cutar daji masu dauke da ita za su iya kare kan su daga kamuwa da ita idan har sun san abin da ya kamata su yi tun da farko bayyanar cutar a jikinsu.

Ya ce a cikin abubuwan da suke kawo cutar daji, akwai hayakin taba (mutanen da suke shan taba kenan) da kuma shan giya wanda wadannan abubuwa sun fi lahani a jikin dan Adam.

Ya kara da cewa kashi 21 bisa 100 na mutane sun fi kamuwa da cutar dajin da ke kama mahaifar mace ta hanyar saduwa da juna domin ita cutar (Human Papilloma Virus) wato cutar da ke haddasa cutar dajin mahaifa shine idan mutum (mace ko namiji) na dauke da shi kuma suka sadu da juna daya daga cikinsu zai iya kamuwa da cutar.

Ya kuma ce mace za ta iya warkewa daga cutar dajin da ke kama mahaifa idan har ta gano cewa ta na dauke da cutar da wuri – wuri ta hanyar yin gwaji da rage yawan mutanen da ake yin jima’I da su wanda hakan yakan iya taimakawa wajen rage yaduwar cutar.

Shugaban kungiyar yace cutar kanjamau da cutar Hepatitis B a turanci kenan na iya kawo cutar daji idan mutum baya shan magani.

Wasu dake fama da cutar sun fadi irin wahalhalun da suke fuskanta saboda suna dauke da cutar;

Samuel Iheine mazaunin jihar Imo yace ya kamu da cutar a shekara 2006 kuma sai da ya tafi kasar Indiya domin samun lafiya bayan ya gagara samun sauki a lokacin da ya kwanta a asibitin jami’ar jihar Legas.

Shi kuma Timothy Terna dan shekara 35 ya ce ya kamu da cutar dajin da ke kama fatar mutum ne a shekarar 2008 inda cutar ta hana shi walwala domin karni da fatar jikinsa take yi.

Ya ce likitoci sun yi masa aikin tiyata guda 8 kenan kuma yanzu haka akwai sauran da suke jiran shi.

Daga karshe shugaban kungiyar ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta yi kokarin karo na’urorin kawar da cutar daji kuma su kara gina asibitocin da mutanen da ke dauke da cutar za su iya zuwa domin samun magani.

Share.

game da Author