Shayar da jarirai nonon uwa na rage mutuwar yara da kashi 13 bisa 100

1

Asusun tallafa wa kanan yara UNICEF, ta shawarci iyaye da su shayar da jariransu nonon uwa na tsawon lokaci domin yin hakan na rage mutuwar yara kanana da kashi 13 cikin 100.

Babban ma’aikaciyar UNICEF Ada Ezeogu ta ce bincike ya nuna cewa jariran da aka dauki tsawon lokaci ana shayar dasu nono sunfi dadewa a duniya akan wadanda ba su sami irin wannan shayarwa ba.

Tace shayar da Jariri nonon uwa na kare da daga kamuwa da cutar gudawa da cututtukar da ya shafi huhu da numfashin jariri.

Ada tace ya kamata a sami watanni 6 ana shayar da yaro nonon uwa kafin a fara tunanin hada mishi da abinci.

Bayan haka kuma ta ce yaro yakan girma cikin kuzari da kaifin basira dalilin haka.

Ada ta fadi haka ne a taron wayar da kai da akayi akan shayar da jarirai nonon uwa, yin rigakafi, da akayi a jihar Ondo, Najeriya.

Share.

game da Author