Mai martaba sarkin Katagum, Alh Muhammad Kabir Umar ya karrama gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar da sarautar Bauran Katagum.
Gwamna Abubakar ne na farko da masarautar za ta karrama da irin wannan sarauta na Baura.
Daya ke sanar da hakan karramawan mai taimaka wa gwamna na musamman akan harkar sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar ya ce sarkin Katagum ya baiwa gwamnan sarautar ne saboda kyakkyawan manufofin da gwamnan ya kirkiro a jihar sannan da inganta jihar da ayyukan cigaba da yake yi.
Sarkin wanda ya tabbatar da mukamin ga gwamnan a wata tawaga da sarkin Azare ya jagoranta daga Katagum, ya bayyana gwamnan a matsayin mutumin da ya ke kokarin ciyar da jihar gaba cikin kankanin lokaci.
Wannan shine karon farko da aka naɗa wani wannan mukamin a jihar Bauchi. An kwaikwayo mukamin ne daga masarautar Sakkwato.
Yayin da yake nuna godiyar sa akan wannan karamci, gwamna MA Abubakar ya kara tabbatar wa mutanen jihar Bauchi da tawagan sarkin Katagum din cewa yana bin sawun marigayi Abubakar Tafawa Balewa da Abubakar Tatari Ali ne, wadanda suka kirkiro jihar.
Gwamnan kuma ya yi godiya ga sarkin Katagum da nuna farincikinsa akan wannan karramawa da masarutar tayi masa.