Shahararren mawakin nan kuma jarumi a harkar fina-finan Hausa Sani Danja ya yi wa matarsa Mansura Isa fatan Alkhairi a murnan zagayowar ranar haihuwanta.
Sani ya rubuta hakanne a shafinsa na Instagram inda ya yabi Mansura da kuma jinjina mata kan kula da take bashi tun bayan aurensu.
Ya roki Allah da ya kara musu lafiya a tsakaninsu sannan ya barsu tare har zuwa tsufarsu.