Shugaban kungiyar kwadugo, Ayuba Wabba ya yi kira ga gwamnati da ta samar wa masu tona asirin barayin gwamnati tsaro ta musamman.
Wabba ya fadi hakan ne a wajen wani tattakin da kungiyar tayi zuwa ma’aikatar lafiya da ke Abuja.
Kungiyar ta gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin jin dadin ta akan sallamar ma’aikata 200 da akayi a asibitin gwamnatin tarayya da ke Owerri saboda tona mata asirin shugaban Asibitin da ma’aikatan sukayi ya kai ga dole ta amsa gaiyatar hukumar EFCC.
Kungiyar Kwadugon tace bai kamata ace an salami ma’aikatan ba saboda kawai sun tona asirin shugaban su.
Ayuba Wabba yace dole ne fa a kirkiro wata doka da zata kare irin wadannan mutanen.
Shugaban kungiyar ya yi bayanin cewa suna da labarin inda aka yi wa dansu barazanar kashe su wasu kuma aka tozartasu saboda sun tona wani abu da ba daidai ba.
Wabba ya ce bai kamata a maida Angela Uwakem kan aikin ta ba saboda tuhumarta da hukumar EFCC ta keyi a yanzu.
A halin da ake ciki yanzu kungiyar ta dakatar da gudanar da zanga-zangar na tsawon kwanaki 3 domin tattaunawa da sakatariyan ma’aikatar kiwon lafiya Binta Bello ko za’a samu mafita akan wannan matsala.