Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da dan jarida Lukas Binniyat a gaban kuliya saboda zarginsa da akeyi na rubuta labaran karya akan rikicin kudancin Kaduna.
Lucas Binniyat ma’aikacin gidan jaridar Vanguard ne inda a watan Janairu ya rubuta wani labarin karya cewa wai Fulani makiyaya sun kashe wasu daliban makarantar koyar da aikin malanta da ke Gidan Waya.
Bayan wallafa wannan labari da gidan jaridar Vanguard tay binciken da akayi akan hakan ta nuna cewa babu wani dalibin makarantar da aka kashe kuma sunayen da Lucas ya bada cewa wai sune aka kashe sunayen karya ne domin ba bu dalibai masu wadannan sunaye a makarantar.
Bayan haka kuma an gano cewa Fulani basu kai hari a wannan rana da ya ce an kashe daliban ba a kurmin Musa dake yankin kudancin Kaduna din.
Lucas Binniyat ya ce wai dalibin da aka kashe James Joseph ya na karatun koyan aikin jarida ne inda shugaban makarantar yace babu irin wannan fanni a makarantar.
Kotu ta ba da belin Lucas
Dan jarida Lucas ya ce gaskiya ya rubuta kuma ba zai canza bakinsa ba.