Kwamandan ‘Operation LAFIYA DOLE’ a yankin Arewa Maso Gabas Lucky Irabor y ace sojin Najeriya ta kama sama da ‘yan kungiyar Boko Haram 3000 a cikin makonni 3 da suka wuce.
Lucky Irabor yace Bayan haka sun kwato makamai da motocin yaki masu dimbin yawa daga hannu Boko Haram din.
Bayan haka ya kara da cewa yanzu burbudin Boko Haram ne suka rage domin sojin Najeriya ta riga ta ci karfinsu.
Ya kuma nuna ma ‘yan jarida wani dan kungiyar da ya mika wuya wanda abokinsa mai suna Hassan Dan-Guduma ya gaya ma shugabannin Boko Haram cewa yana shirin guduwa sai suka yanke masa hannunsa na dama da kafarsa na hagu sannan suka jefar dashi a wata kwata in da sojojin Najeriya suka ceto shi.
Irabor Ya gode ma ‘yan jarida akan irin goyon bayan da suke ba rundunar sojojin domin samun nasara akan Boko Haram.