Gwamnan jihar Barno Kashim shettima ya ce rashin nuna ko inkula ne da tsohon gwamnan jihar Ali Modu Sherrif yayi akan Boko Haram yasa suka zama abun da suka zamo yanzu.
Kashim Shettima ya fadi hakanne yau a taron tunawa da marigayi Janar Murtala Mohammed.
Ya ce duk da cewa da tsohon gwamna Ali Modu Sherrif yayi wai ‘bai bar wata yankin jihar ko daya a hannu kungoiyar Boko Haram ba’ Shettima yace girman kan SAS ya sa aka kasa samun daidaituwa tsakanin kungiyar Yusuffariiya din da jami’an tsaro a wancan lokacin.
Gwamna shettima ya ce a wancan lokacin jami’an tsaro sun kashe wasu magoya bayan Yusufarriya din su 17 saboda rikicin sanya hular kwano ga masu tukin babura a jihar, gwamnati batayi komai a akai ba, bata ziyarci ‘yan uwan wadanda aka kashe ba sannan bata kafa wata kwamiti domin binciken abunda ya faru don kawo karshen rashin jituwan da ke tsakaninsu kamar yadda gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi a jihar sa .
Daga karshe ya karyata rade-radin da akeyi wai shima yana taimaka wa kungiyar Boko Haram din.
Karanta labarin a shafin mu na turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-W6s