Shugaban hukumar NACA Sani Aliyu ya yi kira ga mutanen da ayi kaffa-kaffa da kai a yayin bukin ranar masoya, wato ‘Valentine’s day’.
Sani Aliyu ya yi gargadi ga masoya da su dawo da ga rakiyar nuna rashin ko inkula da suke yi wa juna musamman a wannan lokaci na ranar soyayya ganin yadda ciwon kanjamau ta zama ruwan dare a kasashenmu.
Sani yace idan har masoya za su sadu da juna kada sumanta da yin amfani da kariya, wato kororo ruba.
Ya shawarci matasa da su nisantar da kansu daga saduwa da juna idan kuma har hakan bazai yiwu ba ya yi kira garesu da su yi amfani da Kororo ruba.
Yace hakan zai kare su daga musamman cutar kanjamau.
Ya roki mutane da su nemi sanin matsayinsu akan cutar kanjamau wajen yin gwaji saboda hakan zai tai maka wajen rage yaduwar cutar da wadansu cututtukan da ake kamawa ta hanyar saduwar namiji da mace.