Oba Akiolu na Legas bai Isa ya hana Atiku takara a Najeriya ba – Inji NEF da ATT

0

Kungiyoyin NEF da na ATT sun nuna bacin ransu kan maganganun da Sarkin Legas Oba Rilwanu Akiolu yayi akan tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar.

Oba Rilwanu ya ce mutanen Najeriya ba za su sake yarda irin su Atiku da basu san darajar dukiyan jama’a ba su rike kasa Najeriya kuma ba.

Ya ce ya ji kishin-kishin din cewa Atiku na shirin sake fara neman shugabancin kasa Najeriya, ” Hakan ba zai taba yiwuwa ba domin da kai na zan fito domin nuna adawa akan wannan shiri na ka”

Oba ya fadi hakanne a wata taro da akayi a jihar Legas ranar Laraba.

A wata martani da wasu kungiyoyi biyu suka mai da wa Oba, kungiyar NEF da ATT sun ce Oban bai Isa ya sa ko ya hana Atiku takara a kasa Najeriya ba.

Shugabannin kungiyoyin Abdulaziz na NEF da Danlami DanAsabe na ATT duk sun yi kira ga Oba da ya shiga taitayinsa domin shi kansa ba mutumin kirki bane musamman ganin yadda ya zama sarkin Legas ta hanyar murdiya wanda duk sun san hakan.

Sunce ko a siyasar Legas shi ba komai bane ballantana siyasar kasa Najeriya.

Sun ce Atiku goyon bayan jama’a yake nema ba irin na su ba da ba za tayi wata tasiri ba a wajensa.

Share.

game da Author