Najeriya za ta fara sarrafa kashi 70 bisa 100 na magungunan da take bukata

0

Gwamnatin tarayya ta sanarwa kamfanonin dake sarrafa magunguna a kasa Najeriya cewa a shirye take domin bata duk wata taimako da take bukata domin samun nasarar aikinta kan burin kasa na iya sarrafa kashi 70 bisa 100 na magungunan da mutanen kasa za su bukata a duk shekara.

Da yake zantawa da  manema labarai ministan kiwon lafiya Isaac Adewole yace sun samu daidaituwa akan hakan ne bayan ganawa dasu kayi da kungiyar kamfanonin sarrafa magunguna mai suna Manufacturers Association of Nigeria (PMG-MAN) a Abuja.

Ministan yace sun yi haka ne domin mutane kasa su sami sahihan magunguna sannan kuma musu sauki.

Ministan yace sun kafa wata kwamitin kwarraru wanda shugaban hukumar NAFADAC Modupe Chukuma zai shugabanta domin su taimaka wurin zakulo da magungunan da kamfanonin sarrafa magunguna na Najeriya ba su iya sarrafa su ba.

Yace Idan har aka samu nasaran yin hakan za’a samu sauki wajen irin makudan kudin da kasa take kashewa wajen biyan haraji da kasa ke biya idan za ta shigo da magungunan daga kasashen waje.

Ya kuma shawarci shugabanin kamfanonin da su tabbatar da cewa magungunan da za su sarrafa na da sauki wurin siya sannan kuma kowa zai iya samu a ko’ina.

Daga karshe ministan Isaac yace gwamnatin Najeriya za ta ware wasu kudaden a cikin kasafin kudin 2017 domin ta taimakawa kiwon lafiyar ‘yan Najeriya da ke zama a kasashen waje.

Share.

game da Author