Najeriya na daga cikin kasashe 3 da kananan yara ke fama da matsanancin yunwa

1

Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta ce a wannan shekara kasa Najeriya da wasu kasashen duniya uku, Yemen, Somalia da Sudan ta kudu za su yi fama da ibtila’I na yunwa.

UNICEF ta ce a bayanan da ta samu kan wani bincike da ta gudanar yara miliyan 1.4 na fama da yunwa a kasashen wanda hakan zai iya sa a rasa rayukan yaran.

Bayanan binciken ya bada adadin yara 462,000 na fama da yunwa mai tsanani a kasar Yemen sanan kasa Najeriya na bi mata da adadin yaran masu fama da yunwa har 450,000.

Kasar Somalia it ace ta uku a jerinsu kasashen inda adadin yara dake fama da yunwa ya kai har 185,000 duk da a hakan ma ana kyautata zaton cewa yawan yaran zai iya karuwa zuwa 270,000.

Wani darektan a UNICEF Anthony Lake ya yi kira ga gwamnatocin kasashen da su dauki matakin gaggawa domin shawo kan wannan fitana da ke neman ya hallaka yara kanana a kasashensu.

Share.

game da Author