Mutane 14 ne aka kashe a wata sabuwar hari da aka kai kudancin Kaduna

0

Wadansu da ba’a san ko su waye ba dauke da makamai sun kai hari wasu kauyuka da ke kananan hukumomin Jema’a da Kaura da ke jihar Kaduna, inda suka kashe akalla mutane 14 sannan suka Kona gidajen mazauna garuruwan da gonakinsu.

Bincike ya nuna cewa mata da yara ne abun ya fi shafa.

An kai hare-haren ne a cikin daren jiya zuwa safiyar litinin din nan.

Jami’an tsaro sun kashe mutum daya cikin wadanda suka kai hare-haren, sannan an
ajiye gawawwakin wadanda aka kashe a babban asibitin gwamnatin dake Kafanchan.

Tuni dai gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasiru El-Rufai ya umurci kwamandan rundunar soji dake Kaduna Ismaila Isa da Sifeton ‘yan sandan jihar Agyole Abeh da su koma da ofisoshinsu yankin kudancin Kaduna din domin ci gaba samar da tsaro a yankin.

El-Rufai ya roki jama’ar yankin da su zauna lafiya da Juna sannan su cigaba da mara wa gwamnati baya domin ganin ta cimma burinta na samar da zaman lafiya a yankin.

Daga karshe gwamnan ya yi Allah wadaran wadanda suke ruruta wutan wannan kashe-kashe a yankin jihar.

Share.

game da Author