Kungiyar Jama’atu za ta ba gwamnatin jihar kaduna duk wata goyon baya da take nema 100 bisa 100 domin a hukunta duk wanda aka samu ko aka kama da hannu a rikicin kudancin Kaduna.
Sakataren kungiyar Ibrahim Kufaina yace babu wata addini da yace ka kashe dan uwanka wai don ba addininku daya ba.
Yace suna goyon bayan gwamnan jihar 100 bisa 100 akan yadda take kokarin kawo karshen wannan tashin hankali da yaki ci yaki cinyewa a jihar.
Sakataren kungiyar Kiristocin jihar Kaduna Sunday Ibrahim ya roki yan uwansa limamen coci da su daina ingiza mabiyansu wajen daukan fansa akan abubuwan da ya faru.
Yace kungiyar na goyon bayan matakin da gwamnan jihar ya dauka domin hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikicin kudancin Kaduna.
Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan da ya jagoranci tawagar gwamnatin zuwa ofisoshin shugabannin addinan yace gwamnatin jihar ba za tayi kas-kasa ba wajen ganin ta wadata mutanen jihar da abubuwan more rayuwa ba sannan ta na rokon jama’a da su zauna lafiya a tsakaninsu.
Discussion about this post