Tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema yace gwamnan jihar Aminu Bello Masari na bibiyan rayuwarsa tun bayan zamansa gwamnan jihar.
Ibrahim Shema yace Masari na yin amfani da kujeransa na gwamna domin ci masa mutunci sannan da yin barazana ga lafiyarsa da rayuwarsa.
Shema yace gwamna Masari na yin amfani da jami’an hukumar EFCC domin ci masa mutunci.
Mataimaka wa gwamna Masari akan harkar watsa labarai, Abdu Labaran yace babu ruwan Masari da matsalar da Shema ya shiga. Yace idan har yana neman wanda zai zarga ne toh ya duba madubi zai ga wanda yake bibiyan rayuwarsa.
Yace babu ruwan Masari da badakalar da shi Shema ya shiga.
Yace bai ga dalilin da zai sa tsohon gwamnan jihar yace wai kotu da aka kaishi ya na damunsa ba, bayan shi ne da kansa yake fadi a gidajen rediyo cewa idan akwai abunda gwamati ke nema a wurinsa ta kaishi kotu.
Labaran Abdu yace jama’a su sani cewa babu hannun gwamna Masari acikin matsalar da tsohon gwamna Masari ya shiga.