Kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya NUAHP sun yi wa gwamnati barazanar shiga yajin aiki daga ranar 27 ga watan Fabrairu saboda rashin ko in kula da ta ke nuna wa akan alkawuran da ta dauka na gyara matsalolin da fannin kiwon lafiya ke fama da shi.
kungiyar ta fadi hakanne ranar Litinin din da ya gabata yayin da ta yi tattaki a titunan Abuja.
Shugaban kungiyar Obonna Obinna yace dalilin da ya sa suka fito titunan Abuja shine domin su nuna fushinsu ga gwamnati.
Bayan haka wannan zanga –zangar itace karo ta uku a cikin wannan watan da kungiyar suke fito wa.
Obinna ya ce gwamnatin Najeriya ta kasa gyara asibitocin kasan inda aka kyale mutane na mutuwa saboda rashin wadata su ingantacciyar kiwon lafiya sannan su kuma manyan kasa suna fita kasashen waje domin samun kula da kudin harajin ‘yan Najeriya.
Ya kuma ce idan da sun gyara asibitocin kasan da basa su dunga fita kasashen waje neman lafiyarsu ba.
Discussion about this post