Kungiyar Kwallon kafa ta Leicester city ta salami mai horas da ‘yen wasanta Claudio Ranieri.
Kungiyar ta sanar da hakanne yau a shafin ta da ke yanar gizo.
Kungiyar Leicester ce ta lashe gasar Premier league a kasar Ingila a shekarar da ta gabata.
A wannan shekara kungiyar na ta fama da rashin nasara a wasanninta inda ta take kusa da na karshe a jerin kungiyin da suke fafatawa a kasar.