Kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa Athletico Madrid da ci 2 da1

0

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta doke takwaranta ta Athletico Madrid da ci biyu da daya a gasar kwallon kafa na cin kofin kungiyoyin kwallon kafa na kasar Spain mai suna Copa Delray.

Barcelona ta ci kwallonta na farko ne ta hannun dan wasanta mai buga mata lambs 9 wato Luis Suarez minti 7 da fara wasan.

Shahararren dan wasan kungiyar Leo Messi ya saka wa Athletico kwallo ta biyu a cikin minti 33.

Griezzman ya ramo kwallo daya wa Athletico Madrid kafin cikan lokaci bayan andawo daga hutun Rabin lokaci.

An tashi wasan dai Barcelona na da ci 2 Athletico Madrid na da ci 1.

Share.

game da Author