Ko da yake wasan tayi armashi duk da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bi Alaves gida ne ta samu nasaran saka mata kwallaye 6 babu ko daya.
Daya daga cikin mai tsaron bayan Barcelona, Aleix Vidal ya samu targade a hannunsa inda sakamakon likitocin Barcelona ya nuna cewa dan wasan bazai sake iya buga kwallo bana ba.
A sanarwar da likitocin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fitar, Vidal zai yi jinyar targadensa har na tsawon watanni biyar wanda hakan ya wuce sauran kwankin da suka rage a wasannin bana.
Itama Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta lallasa Osasuna da ci 3 – 1.
A kasar Ingila kuma, Kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea ta buga kunni doki da Burnley da ci 1-1, ita kuma Arsenal ta doke Hull City da ci 2 da nema.
Ga sakamakon yadda ta kaya a Najeriya
Sunshine Stars 2-2 ABS FC
Lobi Stars 0-0 Katsina United
Elkanemi Warriors 3-0 Gombe United
Niger Tornadoes 1-0 Enyimba FC
Nasarawa United 3-1 Abia Warriors
Akwa United 2-1 Plateau United