Ku taya Buhari da addu’a ne maimakon mutuwa da kuke kira masa – Hajiya Rakiya

0

‘Yar uwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari Hajia Rakiya Adamu ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da yi ma shugaban kasa addu’ar samun lafiya.

Hajiya Rakiya ta ce idan Allah ya so ya dora wa mutum ciwo babu wanda zai iya hanawa haka kuma idan ransa ma zai dauka babu wanda ya isa ya hana hakan.

Ta kara da cewa mai makon mutuwa da ake kira masa, addu’a ya kamata a yi masa domin ya sami sauki.

Tace a kullum sai tayi magana da dan uwanta Muhammadu Buhari kuma ta na da yakinin yana nan lafiya.

Hajiya Rakiya ta kara da cewa su 28 ne a dakinsu amma yanzu saura su biyu suka rage a duniya.

Ta roki ‘yan Najeriya da su taya shugaban kasan da addu’a mai makon fatan mutuwa da akeyi masa.

Share.

game da Author