Hukumar kula da safarar jiragen kasa ta kasa ta sanar da kara kudin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja.
Shugaban hukumar Fidet Okhiria yace an yi hakanne domin asamu daidaituwa wajen samun kudin shiga wa hukumar.
Yace karamar kujera wanda take naira 600 ta koma 1,050, inda babban kujera kuma ta koma 1500 daga 900.
Fidet Okhiria ya kara da cewa dama can kudaden ake biya domin shiga jirgin ta gwaji ne ba tabbatacciya bace.
Ya koka da yadda man jirgin kasan ya tashi inda hakan na daga cikin dalilan da yasa dole su dan kara kudin jirgin.
Daga karshe ya ce hukumar na sauraren wadansu sabbin taragon jirgin kasan kafin karshen wannan shekara.