Babban likita a asibitin koyarwa da ke garin Ilori, jihar Kwara Dupe Ademola-Popoola ta yi tsokaci akan yadda iyaye zasu kare ‘ya’yansu daga kamuwa daga cutar makanta.
Ta ba da wadannan bayanai ne a taron da aka shirya domin yin gwajin cutar ciwon ido a asibitin gwamnatin dake Igboro a Ilori.
Ta ce a wata binciken da ta gudanar ta gano cewa iyayen yaran da suka kamu da cutar makanta sukan boye su a gidajensu har sai sun yi girman da za su iya fita bara.
Likita Popoola ta ce gwamnatin jihar ta kafa wata doka da zai tilasta wa iyayen kananan yara daga shekara biyar zuwa kasa da su kai su asibitoci domin gwajin cutar makanta kafin su saka su a makaranta.
Domin mara wa wannan shiri na gwamnati baya, hukumar USAID ta tallafawa gwamnatin jihar da na’urorin gwajin ciwon ido.
Malama Popoola ta ce gwamati ta kardamar da asibitoci 4 domin gwajin masu dauke da cutar makanta da kuma gwaji ga yara kanana.
Bayan haka kuma wadannan asibitoci za su zamo makaranta ga malaman asibiti domin koyar da yadda za’a kula da yara kanana musamman wadanda suke dauke da cutar makantarda kuma neman gwaji idanu akan hakan.
Uwar gidan gwamnan jihar Omolewa Ahmed ta jinjina wa gwamnatin jihar da kirkiro da irin wannan doka sannan kuma ta roki iyaye mata da su mara wa mata baya domin samun nasara akan kokarin da ta keyi na ganin ta kau da cutar makanta a jihar.