Kada kiristoci suyi watsi da Buhari, kowa ya sashi a Addu’a – Inji Shugaban CAN

0

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN ya yi kira ga kiristocin Najeriya da kada su yi watsi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, su ci gaba da yi masa addu’ar samun lafiya har sai ya dawo kasa Najeriya.

Kakakin shugaban kungiyar CAN din Adebayo Oladeji ne ya sanar da hakan a wata sako daga shugaban kungiyar Olasupo Ayokunle.

Ya roki mabiya addinin kirista da su dage da yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari Addu’a har sai ya dawo kasa Najeriya cikin koshin lafiya.

Ya kuma yi kira ga mutane da su kwantar da hankalinsu kan korafe-korafen da ake ta yadawa wai rashin Buhari ya sa kujeran mulki na rawa. Yace kowa ya kwantar da hankalinsa domin Buhari yayi abinda ya kamata na mika wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ragamar mulkin Najeriya zuwa har ya dawo. Sannan yace yana da yakinin cewa mataimakin shugaban kasan zai iya rike kujeran har Buhari ya dawo.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su yi kokarin ganin an kawo karshen rikicin da ake ta fama dashi a yankin kudancin Kaduna.

Share.

game da Author