Sakamakon zaben kananan hukumomi da akayi a jihar Taraba ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce ta lashe kujerun duka kananan hukumomin jihar.
Ko da yake har yanzu ana jiran sakamakon zaben kananan hukumomin Sardauna da Karin Lamido PDP ce ta lashe sauran.
An soke zaben karamar hukumar Ibi.
Ga sunayen wadanda suka lashe kujerun kananan hukumomin
Mohammed Umar Gashaka, Nicholas Waniyafiwani, Lau; Abdul Boboji, Jalingo; Danladi Suntai Bali,
Salisu Dogo, Ardo-Kola; Joseph Mika, Yorro; Mr Adi Daniel, Wukari, Christopher Koshombo, Zing; Yahuza Yahaya, Gassol; da Nashuka Musa,Donga.
Sauran sun hada da Shiban Tikari, Takum; Stephen Agya, Kurmi; da Rimansikwe Karma, karamar hukumar Ussa.