Jam’iyyar PDP ta ce bata amince da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ba na tabbatarwa Ali Modu Sherrif kujeran shugabancin jam’iyyar.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose yace bangarensa (Magoya bayan Makarfi) ba ta yarda da hukuncin ba saboda haka za ta garzaya kotun koli domin daukaka kara.
Mabiya jam’iyyar na bangaren tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi sun zargi jam’iyyar APC da yi musu bita da kulli akan wannan shari’a.
PDP tace Jam’iyyar APC na yi mata zagon kasa a wannan rikici na shugabancin jam’iyyar.