Kungiyar Jama’atu Nasrul-Islam JNI reshen jihar Jigawa ta gudanar da addu’o’I ta musamman ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
An gudanar da Addu’o’in ne a garin Miga dake jihar Jigawa.
Sakataren Kungiyar na reshen jihar Jigawa Muhammad Babangida yace sun gudanar da addu’o’in ne domin nema wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari Lafiya da kuma kasa baki daya.
Masallatai a jihar Jigawa ne suka gudanar da addu’o’in ranar juma’ar da ta gabata.