Hukumar tantance fina-finai ta jihar Kano ta maka Sadiq Zazzabi a kotu

0

Gwamnatin jihar Kano ta maka shahararren mawakin Hausa nan Sadiq Zazzabi a kotu saboda zargin karya dokar hukumar tantance fina-finai ta jihar Kano.

Zazzabi ya na zargin hukumar da neman muzguna masa saboda yayi wa Kwankwaso waka ne bawai don ya karya wata doka ba.

Da yake tattaunawa da gidan jaridar PREMIUM TIMES kan sammacin Sadiq yace ya mika wakar tasa ga hukumar tantance fina-finai ta Kano tun 6 ga watan Janairu domin a bashi izinin fitar da wakar amma hakan ya gagara har yanzu.

Yace bayan haka kuma hukumar SSS ta gaiyace shi da ya zo yayi mata bayani akan wakan.

“Bayan amsa gaiyatar SSS, na yi musu bayani akan abin da wakar ta kunsa kafin suka sallameni.

A takardar gaiyatar wanda wannan gidan jarida PREMIUM TIMES HAUSA ta gani ana bukatar Sadiq ya zo kotun hukumar tantance finafinai ne dake gidan Audu Bako a Kano gobe domin ba da bayanai akan dalilin da yasa ya saki wakar ba tare da samun ikon yin hakan ba daga hukumar.

Shugaban hukumar Isma’ila Afakallahu ya sanar ma wannan gidan jarida cewa mawakin ya saba dokar hukumar shine ya sa suke gaiyatarsa domin ya bada bayanai akan abinda yasa yaki jiran hukumar ta amince masa da ya saki wakar kawai yayi awon gabansa.

Share.

game da Author