Babban jami’a a ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa Ramatu Hassan ta ce gwamnatin Najeriya na fama da rashin kwararrun injiniyoyin da zasu duba da gyara na’urorin kawar da cutar daji idan suka samu matsala a cibiyon kiwon lafiya da asibitocin kasar nan.
Ta ce rashin kwararrun da za su duba wadannan na’urori babban matsala ce a kasa Najeriya musamman yadda kasar ke kokarin ganin ta kawar da cutar dajin da yake addabar mutane yanzu haka.
Bayan haka ta ce ma’aikatan kiwon lafiya ta kafa wata kwamiti wanda ministan kiwon lafiya Isaac Adewole zai jagoranta domin daukaka darajar asibitocin da ke kula da masu dauke da cutar dajin da kuma gina sabbin asbitoci domin maganin cutar. Ma’aikatar za ta hada hannu da babban bankin duniya da kungiyar agaji na Red Cross domin samun nasar akan hakan.
Malama Ramatu tace mafi yawancin asibitocin da suke kula da marasa lafiyar da ke dauke da cutar daji a kasa Najeriya basu aiki a halin yanzu.
Ta kawo misali da asibitocin da ke garuwan Maiduguri, Zaria, Ilori, Abuja, Ibadan, Benin da Enugu cewa duk basa aiki a yanzu hakan.
“ Asibitin koyarwa ta jami’ar Usman danfodio da ke Sokoto na aiki yadda yakamata musamman wajen kula da masu dauke da cutar daji din.” Ramatu tace.
A dalilin hakan kuma Malama Ramatu tace za’a gina sababbin asibitoci domin kula da warkar da masu dauke da cutar guda bakwai a kasa Najeriya a wannan shekara sannan a gina wadansu 7 a shekara mai zuwa.
Daga karshe tayi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka domin ganin cewa an samu nasara akan wannan aiki da aka sa a gaba.