Ministan kiwon lafiya Isaac Adebowale ya ce gwamnati za ta tantance ingancin maganin warkar da cutar kanjamau da wani farfesa mai suna Maduike Ezeibe ya ce ya gano.
Ministan ya ce dalilin yin hakan kuwa shine domin a tabbatar da ingancin maganin ta hanyar yin gwaji kafin mutane su fara amfani da shi.
Ya Kara da cewa samun maganin warkar da cutar kanjamau zai taimaka wa mutanen da ke dauke da cutar a kasa Najeriya wajen samun sauki da warkewa daga cutar.
Najeriya ta na daga cikin jerin kasashen da suke da yawan mutanen da ke dauke da cutar Kanjamau. Itace ta biyu bayan kasar Afrika ta kudu a yawan mutanen da ke dauke da cutar a nahiyar Afrika.
Adebowale ya kara da cewa da zaran an kammala bincike da tantance ingancin maganin ma’aikatarsa za ta sanarwa mutane sakamako binciken da matsayin gwamnati akai.
Da yake magana akan cibiyoyin kiwon lafiya, Adewole yace gwamnati na gab da cika alkawuran da ta dauka na gyara cibiyoyin kiwon lafiya guda 10,000 a kasa Najeriya a wannan shekara.
Ya ce kungiyar hadin kan kasashen turai ‘European Union’ za ta zuba jari a cibiyoyin kiwon lafiya 650 sannan kuma za ta taimaka wajen gyaran cibiyoyin kiwon lafiya 950 a kasa Najeriya.
Discussion about this post