Gwamnatin tarayya ta na da wata kwamiti ta musamman domin duba yadda farashin kayan abinci yake ta hau-hawa a kasuwannin kasar nan.
Ministan watsa labarai Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnati.
Lai Mohammed ya ce gwammnati ta damu akan yadda kayyayyakin abinci k e tashin gauron zabi a kasuwannin kasarnan saboda haka ne ta kafa wannan kwamti domin ta duba sannan ta bata shawara akan abinda ta ga ya dace ayi domin samar wa mutane sauki akan hakan.
“Babban abin da kwamitin za tayi shine ta duba inda gwamnati zata kawo dauki akan hau-hawan farashin kayayyakin abincin domin samar wa mutane sauki. Daukin zai iya zama ta hanyoyi kamar Safarar kayan abincin wanda hakan yakan sa suyi tsada a kasuwanni.
Ministan Ayyukan gona, Kudi, sufuri da ruwansha ne aka wakilta domin su duba hakan.
Zasu mika rahotansu a taron majalisar zartaswa na makon gobe.